Colossians 3

1Idan dai Allah ya tashe ku tare da Almasihu, ku nemi abubuwan da ke sama, inda Almasihu ke zaune a hannun dama na Allah. 2Yi tunanin a kan abubuwan da ke sama, ba a kan abubuwan da ke kasa ba. 3Gama ku kun mutu, ranku kuma yana boye tare da Almasihu cikin Allah. 4Sa’anda Almasihu ya bayyana, wanda shine ranku, sa’anan ku kuma zaku bayyana tare da shi cikin daukakarsa.

5Ku kashe sha‘awacce-sha’awaccen da suke a duniya - zina da fasikanci, rashin tsarki, muguwar sha’awa, mummunar buri, da kuma kwadayi, wadda shine bautar gumaka. 6Saboda wandannan abubuwa ne fushin Allah ke zuwa a kan marasa biyayya. 7A cikin wadannan abubuwa ne kuka yi rayuwa a da da kuke zauna a cikinsu. 8Amma yanzu dole ku kawar da wadannan - zafin rai, fushi, mugayen manufofi, zage-zage, da kazamar magana daga bakinku.

9Kada ku yi wa juna karya, domin kun tube tsohon mutumin da ayyukansa, 10kun kuma yafa sabon mutum, wanda ake sabontawa cikin sani bisa ga surar wannan da ya hallice shi. 11A nan ne inda babu Baheline da Bayahude, mai kaciya da marar kaciya, bare, baubawa, ko Basikitiye, bawa ko yantacce, amma Almasihu shine duka, yana kuma cikin duka.

12A matsayin ku na zababbun Allah, masu tsarki da kaunatattu sai ku yafa jinkai, ayyukan kirki, saukin kai, kamewa da hakuri. 13Yi hakuri da juna. Ku yi wa juna alheri. Idan wani na da damuwa da wani, ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku. 14Fiye da wadanan abubuwa duka, ku kasance da kauna, wanda itace cikakkiyar kammalla.

15Bari salamar Almasihu ta mallaki zukatanku. Sabili da wannan salama ce aka kiraye ku cikin jiki daya. Ku yi godiya. 16Ku bar maganar Almasihu ta zauna a cikinku a yalwace. Da dukan hikima, ku koyar, ku kuma gargadi juna da zabura, wakoki, da wakokin yabo na ruhaniya. Kuna rairawa tare da godiya cikin zukatanku ga Allah. 17Kuma duk abin da zaku yi cikin magana ko aiki ku yi duka cikin sunan Ubangiji Yesu. Kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

18Mata, ku yi biyayya ga mazajenku, yadda yakamata a cikin Ubangiji. 19Mazaje, ku kaunaci matayenku, kada ku muzguna masu. 20Yaya, ku yi wa iyayen ku biyayya cikin dukan komai, domin wannan yana faranta wa Ubangiji rai. 21Ku Ubanni, kada ku cakuni ‘ya’yanku domin kada su karaya.

22Bayi, ku yi wa iyayengijinku na jiki biyayya cikin kowane abu, ba tare da bautan ganin ido ba don faranta wa mutane rai, amma da sahihiyar zuciya. Ji tsoron Ubangiji. 23Duk abin da kuke yi, ku yi aiki daga zuci domin Ubangiji ba domin mutane ba. 24Kun san cewa, zaku karbi sakamako na gado daga wurin Ubangiji. Domin Ubangiji Almasihu kuke bauta wa. Domin kowa ya yi rashin adalci zai karbi sakamakon rashin adalcin da ya yi, kuma babu son kai.

25

Copyright information for HauULB